1 John 4

1Kaunatattu, kada ku amince da kowanne ruhu. Amma ku gwada ruhohi ku gani ko na Allah ne, gama annabawan karya masu yawa sun fito zuwa cikin duniya. 2Ta haka zaku gane Ruhun Allah, dukkan ruhun da ya amince Yesu Almasihu ya zo cikin jiki na Allah ne, 3kuma dukkan ruhun da bai amince da Yesu ba, ba na Allah bane. Wannan ruhun magafcin Almasihu ne, wanda kuka ji cewa yana zuwa, ya kuwa rigaya yazo cikin duniya.

4‘Ya’yana kaunatattu, daga Allah ke, kuma kun rigaya kun yi nasara da su da yake wanda ke cikinku ya fi wanda ke cikin duniya girma. 5Su na duniya ne, saboda haka abin da suke fadi na duniya ne, duniya kuma tana sauraronsu. 6Mu na Allah ne, duk wanda ya san Allah yana saurarenmu. Wanda ba na Allah bane, ba ya sauraronmu. Ta haka muka gane ruhun gaskiya da ruhun karya.

7Kaunatattu, mu yi kaunar juna, gama kauna ta Allah ce, wanda yake kauna an haife shi daga wurin Allah, kuma ya san Allah. 8Mutumin da baya kauna ba na Allah ba ne, kuma bai san Allah ba, gama Allah kauna ne.

9A cikn haka aka bayyana kaunar Allah a garemu, Allah ya aiko tilon Dansa cikin duniya domin mu rayu ta wurinsa. 10A cikin wannan akwai kauna, ba mune muka kaunaci Allah ba, amma shi ya kaunace mu ya aiko da Dansa ya zama mai gafarta zunubanmu.

11Kaunatattu, da yake Allah ya kaunace mu haka, ya kamata mu kaunaci junanmu. 12Ba wanda ya taba ganin Allah. Idan muna kaunar juna, Allah yana zaune cikinmu, kuma kaunarsa tana zaune a cikinmu. 13Ta haka mun sani muna zaune a cikinsa shi kuma a cikinmu, saboda ya bamu Ruhunsa. 14Mun gani mun shaida, cewa Allah ya aiko Dan, domin ya zama mai ceton duniya.

15Duk wanda ya amince Yesu Dan Allah ne, Allah na zaune cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Mun sani kuma mun gaskata da kaunar da Allah yake da ita dominmu, Allah kauna ne wanda yake zama cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma a cikinsa.

17Dalilin wannan kauna ta kammala a cikinmu, domin mu kasance da gabagadi a ranar shari’a, domin kamar yanda ya ke haka muma muke a cikin duniyan nan. 18Babu tsoro a cikin kauna. Amma cikkakiyar kauna takan kawar da tsoro, domin kuwa tsoro na tafi tare da hukunci. Amma wanda yake da tsoro ba shi da cikkakiyar kauna.

19Muna kauna domin Allah ne ya fara kaunarmu. 20Idan wani ya ce,”Ina kaunar Allah”, amma yana kin dan’uwansa, makaryaci ne. Domin wanda baya kaunar dan’uwansa da yake gani, ba zai iya kaunar Allah da bai taba gani ba. Wannan ne umarnin da muke da shi daga wurinsa: Duk wanda yake kaunar Allah dole ne ya kaunaci dan’uwansa.

21

Copyright information for HauULB